Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun sace dalibai da malaman Kwalejin Nuhu Bamali dake Zaria

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria

Rahotanni daga jihar Kaduna dake Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kasha mutum guda, yayin da kuma suka sace wani adadi na malamai da dalibansu daga Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Nuhu bamali dake garin Zaria.

Talla

Bayanai sun ce lamarin ya auku ne a daren ranar Alhamis inda ‘yan bindigar suka sace akalla malamai Kwalejin Fasahar 2, sai dai babu karin bayani kan yawan daliban da maharan suka sace ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ‘yan bindiga ke kai hari kan manyan makarantu tare sace dalibansu a jihar Kaduna ba, inda a cikin watan Afrilu suka sace daliban jami’ar Greenfield dake karamar hukumar Chikun, sai kuma a ranar 11 ga watan Maris da wasu ‘yan bindigar suka sace daliban kwalejin horas da malaman kula da gandun daji dake karamar hukumar Igabi.

Satar daliban na Kaduna a baya bayan nan, na zuwa ne a yayin da ake tsaka da alhinin daliban Islamiyya yara da malamansu sama da 100 da ‘yan bindiga ke cigaba da yin garkuwa da su a jihar Neja bayan sace su daga garion Tegina.

A baya bayan nan ne dai yayin wata hira da kafar talabijin ta Arise TV shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe masu ta’addancin da suka addabi sassan kasar nan ba da jimawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI