Najeriya - Kaduna

An rufe Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli bayan harin 'yan bindiga

Wani sashi na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna.
Wani sashi na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna. © nubapoly.edu.ng

Gwamnatin Kaduna a Najeriya ta rufe Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria, sakamakon sace dalibai da dama da kuma wasu malamai da ‘yan bindiga suka yi daga Kwalejin a daren Alhamis din da ta gabata.

Talla

Har yanzu dai babu karin bayani ainahin adadin dalibai da kuma malaman makarantar Kwalejin Kimiyyar da maharan suka yi awon gaba da su.

Wata daliba da ta tsallake rijiya da baya ta ce 'yan bindigar sun kyale ta ne sakamakon yaranta da take dauke da su, abinda ya sanya ta kasa tafiya da sauri a lokacin da suke kokarin kora su zuwa cikin daji.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ‘yan bindiga ke kai hari kan manyan makarantu tare sace dalibansu a jihar Kaduna ba, inda a cikin watan Afrilu suka sace daliban jami’ar Greenfield dake karamar hukumar Chikun, sai kuma a ranar 11 ga watan Maris da wasu ‘yan bindigar suka sace daliban Kwalejin horas da malaman kula da gandun daji dake karamar hukumar Igabi.

Satar daliban na Kaduna a baya bayan nan, na zuwa ne a yayin da ake tsaka da alhinin daliban Islamiyya yara da malamansu sama da 100 da ‘yan bindiga ke cigaba da yin garkuwa da su a jihar Neja bayan sace su daga garin Tegina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI