NAJERIYA-TSARO

Sojojin Najeriya sama da dubu 7 suka jikkata wajen yaki da Boko Haram

Wasu sojojin Najeriya a Jihar Borno mai fama da matsalar tsaro
Wasu sojojin Najeriya a Jihar Borno mai fama da matsalar tsaro REUTERS/Tim Cocks

Rundunar Sojin Najeriya tace dakarun ta 7,403 ne suka samu raunuka daban daban sakamakon yaki da Boko Haram aka kuma kula da su a asibitin sojin dake Kaduna, yayin da wasu daga cikin su suka rasa rayukan su wajen kare kasar.

Talla

Daraktan kula da asibitin soji da ake kira 44 dake Kaduna Kanal Stephen Onuchukwu ya bayyana haka lokacin da ya karbi tawagar Majalisar Dattawan kasar a karkashin shugaban ta Sanata Ahmad Lawal da suka je domin duba sojojin da ake kula da su a wurin.

Ziyarar wadda ke cikin jerin bukukuwan da aka shirya na cika shekaru 2 da kafa Majalisar ta 9 ta baiwa Yan Majalisar Dattawan damar ganewa idanun su halin da sojojin kasar ke ciki da raunukan da suka samu da kuma yadda ake kula da su.

Kanar Onuchukwu yace alkaluman da suke da shi ya nuna cewar asibitin su dake Kaduna ya karbi sojoji 7,403 da suka samu raunuka domin kula da lafiyar su, yayin da tuni wasu daga cikin su suka warke suka kuma sake komawa filin daga domin kare lafiyar kasa.

Nigeria Senate President elect, Ahmed Lawan
Nigeria Senate President elect, Ahmed Lawan premiumtimesng
Onuchukwu yace daga cikin wadanda ke samun kula a asibitin yanzu haka akwai wadanda suke fama da matsalar kashin baya da wadanda suka rasa wani sashe na jikin su.

Daraktan yace duk da daga darajar asibitin da kuma fadada shi har yanzu akwai wasu ayyukan da sai an kai kasashen waje, abinda ya sa ya bukaci Majalisar dokokin da gwamnatin tarayya da su hada kai wajen daga darajar asibitin zuwa mataki na 4 kamar na Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. © AFP
Shugaban Majalisar Dattawan Ahmad Lawal yayi alkawarin cewar bangaren majalisar zai hada kai da na zartarwa wajen kula da lafiyar jami’an sojin kasar kamar yadda ya dace.

Sanata Lawal yace majalisar zata gaggauta amincewa da kasafin kudin wucin gadi da shugaban kasa ya gabatar na naira biliyan 895 da ya kunshi kudin sayen kayan soji da kuma maganin rigakafin cutar korona, yayin da za’a kara yawan kudin da za’a baiwa bangaren sojin a kasafin kudin shekara mai zuwa.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. premiumtimesng
Shugaban majalisar yace abin takaici ne yadda ake baiwa sojojin Najeriya ‘yan kudin kadan kuma ake bukatar su da suyi aiki sosai, inda yake cewa sojojin na bukatar goyan bayan kowanne dan Najeriya.

Daga bisani Sanata Lawal ya baiwa asibitin taimakon naira miliyan 10 a madadin Majalisar Dattawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI