Ranar Demokradiya

An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a wasu biranen Najeriya

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Legas.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Legas. © Daily Trust

A Najeriya an gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a wasu manyan biranen kasar, inda ta zama tashin hankali a Abuja da Legas har saida ‘Yan sandan suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa gungunsu.

Talla

Masu zanga-zangar dai sun yi amfani da yau 12 ga watan Yuni dake zama ranar Dimkoradiyya a Najeriya don bayyanawa gwamnati bacin ransu kan gazawar da suke zarginta da yi kan fannonin tattalin arziki da tsaro da kuma tsarin tafiyar da mulkin kasar.

Bayanai sun ce gabannin ranar ta 12 ga watan Yuni da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ware don girmama dan takarar shugabancin kasar M.K.O Abiola da kuma tunawa da nasarar zabensa na 1993 da gwamnatin sojoji ta soke, wasu ‘yan Najeriya suka shirya amfani da damar wajen gudanar da zanga-zanga a fadin kasar.

Sai dai jami’an tsaro na ‘yan sanda sun kasance cikin shirin ko ta kwana inda aka girke su a wuraren da masu zanga-zangar suka shirya taruwa.

Wasu masu zanga-zangar adawa da shugabancin Muhammadu Buhari yayin tunawa da ranar Dimokaradiya ta 12 ga watan Yuni, a birnin Akure dake jihar Ondo.
Wasu masu zanga-zangar adawa da shugabancin Muhammadu Buhari yayin tunawa da ranar Dimokaradiya ta 12 ga watan Yuni, a birnin Akure dake jihar Ondo. © Daily Post Nigeria

Rundunar ‘yan sandan Najeriyar dai na kare matakin tawatsa gungun masu zanga-zangar da cewa, ba su nemi izinin gudanar da tattakin nasu ba, kamar yadda doka ta tanadar.

 

Rahotanni sun ce mutane sun samu fita zanga-zangar a wasu biranen sassan Najeriyar, baya ga Legas da kuma Abuja.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin a Legas, ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2021.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin a Legas, ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2021. REUTERS - TEMILADE ADELAJA

Rahotanni sunce an gudanar da zanga-zangar A jihohin Rivers da Ondo da Ogun da Osun sai kuma Plateau dake arewacin kasar.

Yayin tattakin na 12 ga watan Yunin dai, masu zanga-zangar sun rika daga kwalye dauke da rubuce rubucen adawa da gwamnati mai ci gami da neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda gazawarsa kan magance matsalolin da suka dabaibaye kasar.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin a Abuja, ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2021.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin a Abuja, ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2021. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da suka bayyana kansu a matsayin jagororin zanga-zangar ta baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI