Najeriya - Zamfara

Gwamnan Zamfara ya koka kan tsanantar matsalar tsaro a jiharsa

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle © Twitter / @Bellomatawalle1

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya koka kan yadda matsalar tsaron hare-haren ‘yan bindiga ka kara yin muni cikin yanayi na ban tsoro a jiharsa.

Talla

Gwamnan ya bayyana kaduwar tasa ne a lokacin da yake tabbatar da farmakin da ‘yan bindiga suka kai kan wasu yankunan karamar hukumar Zurmi ciki har da Kadawa, inda maharan suka kasha mutane akalla 51, adadin da zuwa jiya Asabar wasu mazaunan yankin suka ce ya kai 70.

A wani labarin kuma a jiya Asabar Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi Atiku Abubakar Muhammad, tare bada umarnin kaddamar da bincike kan zarge-zargen da ake masa na alaka da ‘yan bindigar da suka addabi sassan jihar ta Zamfara.

Umarnin dakatar da sarkin dai ya biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan sassan karamar hukumar ta Zurmi a baya baya bayan nan, inda suka akshe mutane fiye da 50.

Sanarwar da sakataren gwamnatin Zamfara ya fitar Kabiru Balarabe ta kuma bayyana Alhaji Bello Suleiman (Bunun Kanwa) a matsayin wanda zai maye gurbin Sarkin na Zurmi da aka dakatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.