Najeriya

NDLEA ta kwace kwaleben Codeine dubu 100 a tashar jiragen ruwar Fatakwal

Jami'an hukumar NDLEA lokacin da suka kai samame wani gida, inda suka kame wani dan kasar Chadi da Nijar da miyagun kwayoyi da suke harka da 'yan bindiga
Jami'an hukumar NDLEA lokacin da suka kai samame wani gida, inda suka kame wani dan kasar Chadi da Nijar da miyagun kwayoyi da suke harka da 'yan bindiga © ©dailypost.ng

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke sama da kwalabe dubu 100 na maganin Codeine mai nauyin kilogram 15,325 a tashar jirgin ruwan Onne, dake birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Talla

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana samun wannan nasara ranar Asabar a Abuja.

Baba Femi yace, a ranar Alhamis aka gano haramtaccen kwayar, da aka cushe cikin kwalaye 500 kuma aka boye su a cikin wata kwantena dauke da kayan abinci da aka shigo da su daga kasar Indiya, a tashar ta Onne.

Aikin hadin guiwa

A cewarsa, anyi nasarar ce, a lokacin da suke gudanar da wani aikin hadin gwiwa tare da jami’an hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), da jami’an tsaro na farin kaya (SSS), da hukumar kula da abinci da magunguna ta NAFDAC, da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.