Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun sake sace mutane a Zaria

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutane 12 da ‘yan bindiga suka yi a yankin Kofar Gayan da Kofar Kona dake Zaria.

Talla

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kai harin cikin daren jiya Asabar wayewar asubahin yau lahadi.

Sai dai yayin karin bayani kan halin da ake ciki, ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna Muhd Jilge ya ce an yi nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace, ko da yake bai yi karin haske ko sa da aka biya kudaden fansa ba.

Wannan hari ya zo ne bayan sace wani adadi na dalibai da malamansu da ‘yan bindigar suka yi daga Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Nuhu Bamalli dake garin na Zaria kwanaki uku da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.