Najeriya - Borno

Boko Haram na daukar masu leken asiri da kudi kalilan - Zulum

Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum.
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum. RFI Hausa

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya koka kan yadda kungiyar Boko haram ke amfani abin da bai taka kara ya karya ba na adadin kudi wajen daukar sabbin mayaka da kuma wadanda ke musu aikin leken asiri a sassan jihar.

Talla

Gwamnan ya ce rahotanni da suka tattara da binciken da aka yi, sun nuna cewar mayakan na Boko Haram na amfani da tsakanin naira dubu 5 zuwa dubu 10 domin daukar masu yi musu leken asiri da kuma fasakaurin makamai.

Zulum ya bayyana haka ne a karshen makon da yak are, a yayin da yake gabatar da jawabi kan ranar Dimokaradiyya ta 12 ga watan Yuni da kuma bikin cikarsa shekaru 2 akan mulki.

Gwamnan na Borno ya bayyana matsalar yunwa da tagayyarar da ‘yan gudun hijira suka yi a sassan jihar sa Borno saboda rikicin Boko Haram a matsayin damar da kungiyar ke amfani da ita wajen baiwa mutane taimakon abinci da kudade domin daukar sabbin mayaka da kuma masu leken asiri.

Akwai dai dubban matasa da suka sadaukar da kasu a matsayin dakarun rundunar samar da tsaron sa kai ta Civilian JTF a jihar Borno, wadanda ke taimakawa jami’an tsaron Najeriya wajen yaki da kungiyar boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI