Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun yiwa masarautata kofar rago - Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli
Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli YouTube

Mai martaba Sarkin Zazzau Abassada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan yadda matsalar tsaro ta yiwa masarautarsa dabaibayi.

Talla

Yayin karbar bakuncin tawagar kwamishin tsaron jihar Kaduna da lamurran cikin cikin gida Samuel Aruwan a yau Litinin, Sarkin na Zazzau y ace ‘yan bindiga sun yiwa al’ummarsa kofar rago, abinda ya sanya basa da dama iya yin barci cikin kwanciyar hankali a cikin birnin na Zazzau da kewaye.

Ambassada Ahmad Nuhu Bammali ya ce halin da masarautar Zazzau ke ciki ba abinda za a lamunta bane, ganin yadda suke fama da matsalar ta hare-haren ‘yan bindiga duk da kasancewar hedikwatocin manyan hukumomin tsaron Najeriya a kusa da su.

A baya bayan nan ne dai ‘yan bindiga suka sace wani adadi na dalibai da malamai daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria, kwana uku bayan haka kuma wani gungun ‘yan bindigar suka sace mutane 12 a unguwar Sabuwar Gayan da Kofar Kona a dai garin na Zaria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.