NAJERIYA-CIN HANCI

Ana yiwa rayuwata barazana - Shugaban EFCC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa ta EFCC AbduRashid Bawa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa ta EFCC AbduRashid Bawa © The Guardian Nigeria

Shugaban Hukumar EFCC dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya Abdurashid Bawa yayi zargin cewar yana fuskantar barazanar hallaka shi daga wasu ‘yan kasar saboda ayyukan da hukumar sa ta saka a gaba.

Talla

Wannan zargi daga Bawa ya nuna yadda yaki da hancin da rashawa a Najeriya ke da wahala kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi a makon jiya lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

Bawa wanda ya sha alwashin samun nasarar yaki da cin hanci da rashawar da ya saka a gaba, yace a ‘yan kwanakin da suka gabata ya samu barazana daga wani mutuum wanda Hukumar EFCCn bata gudanar da bincike akan sa.

Shugaban hukumar yace ya karbi wayar wani babban mutuum lokacin da ya ziyarci birnin New York inda mutumin ya shaida masa cewar zai kasha shugaban EFCC, ‘dan yaron nan’.

Bawa yace wannan na daga cikin abinda ke nuna yadda mutanen da suka saci dukiyar talakawa ke yaki da ayyukan da hukumar keyi, yayin da yake cewar yana da yakinin zasu samu nasara akai.

Shugaban EFCC ya kuma ce suna sanya ido akan mutanen dake halarta kudaden haramun daga bangaren ma’aikatan gwamnati da kuma masu zaman kan su a yunkurin da suke na dakile wannan matsalar dake batawa Najeriya suna.

Daga cikin hanyoyin da Bawa yace suke dauka harda amfani da shugabannin addini wajen cigaba da fadakarwa dangane da illar cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.

A watan Fabarairun da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Abdurashid Bawa a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC domin maye gurbin Ibrahim Magu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.