Najeriya-PDP

PDP ta bayyana kaduwarta da bashin Najeriya

Gwamnonin PDP a Najeriya
Gwamnonin PDP a Najeriya © gazettengr

Gwamnoni daga jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, sun yi gargadin cewa, ba mamaki dimbin bashin da gwamnatin kasar ke ciyowa daga ketare ya yi sanadiyyar durkushewar tattalin arzikin kasar baki daya.

Talla

A sanarwar da suka fitar bayan kammala taron da suka gudanar a ranar Litinin a Uyo fadar gwamnatin jihar Akwa Ibom, gwamnonin na PDP, sun ce yanzu haka bashin da gwamnatin ta ciyo ya zarta Naira tiriliyan 36, kuma 80% na kudaden shiga da kasar ke samu ana sake amfani da shi ne domin biyan basusuka, lamarin da ke matsayin illa ga tattalin arzikin kasar.

Taron gwmnonin ya caccaki Babban Bankin Kasar (CBN) kan yadda yake gudanar da ayyukansa da sauran hukumomin tattara kudade na kasar wadanda ya bayyana a matsayin masu karfi fiye da kima.

Kazalika taron ya ce, gwamnatin mai ci ta yanzu ta sukurkuta ribar da Najeriya ta samu a karkashin mulkin Olusegun Obasanjo na PDP, lokacin da kasar ta fice daga kangin basuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI