Najeriya - Tsaro

ISWAP ta saki ma'aikatan agajin da ta kama a Najeriya

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres MAXIM SHEMETOV POOL/AFP/Archivos

Mayakan ISWAP dake Najeriya sun saki mutane 10 da suka yi garkuwa da su cikin su harda ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda 2 bayan an dauki makwanni ana tattaunawa da su.

Talla

Majiyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma wata jami’ar da ya shiga tsakani domin kubutar da mutanen da akayi garkuwa da su tace an kama mutanen ne tsakanin watan Disambar bara da Afrilun bana a Yankin arewa maso gabashin Najeriya dake fama da tashin hankali.

ISWAP da Boko haram kan saki mutanen da suka kama lokaci zuwa lokaci idan an tattauna da su wajen biya musu wasu daga cikin bukatun su a rikicin da aka kwashe sama da shekaru 10 ana fafatawa tsakanin su da dakarun gwamnatin Najeriya wanda yayi sanadiyar kashe mutane kusan 40,000.

Ummu-Kalthum Muhammad shugabar Gidauniyar Kalthum ta zaman lafiya da ta jagorancin tattaunawar kubutar da mutanen ta bayyana cewar su 10 ne aka sake kuma cikin su harda ma’aikatan agaji guda 7.

Jami’ar tace daga cikin mutanen akwai ma’aikacin Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kama a watan Disambar bara da wani ma’aikacin kungiyar Red Cross da ma’aikacin Hukumar Kula da Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kama a watan Janairu.

Bayanai sun ce an kama mutanen guda 3 ne lokacin da mayakan suka kafa wani wurin binciken ababan hawa na bogi a wajen birnin Maiduguri.

Muhammad tace akwai kuma wasu ma’aikatan agaji guda 4 da aka kama a watan Afrilu a garin Dikwa lokacin da mayakan ISWAP suka kai hari sansanin Majalisar Dinkin Duniya tare da wani Limamin Kirista guda da malamin jami’a da kuma wani ma’aikacin gwamnati.

Babu dai wani tabbaci daga bangarorin biyu ko an biya diyya kafin sakin ma’aikatan.

Majalisar Dinkin Duniya ta dade tana bayyana damuwa akan halin da ma’aikatan da aka kama ke ciki da kuma hare haren da ake kaiwa jami’an aikin jinkai inda aka kashe 12 daga cikin su a shekarar 2019 kawai.

Akalla mutane miliyan 2 rikicin boko haram ya tilastawa barin gidajen su domin neman mafaka a wasu garuruwa, yayin da masu aikin jinkai ke kokawa kan yadda suke fuskantar matsalar isa a gare su domin kai musu dauki.

 

Rikicin boko haram da ya fara daga Najeriya ya fantsama zuwa kasashen Nijar da Chadi da kuma Kamaru, abinda ya sa aka kafa rundunar hadin gwuiwa domin yakar masu kai hare haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.