Najeriya-Boko Haram

Buhari ya kaddamar da manyan ayyuka a ziyarar da ya kai Maiduguri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ziyararsa a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ziyararsa a birnin Maiduguri na jihar Borno. © Presidency / Garba Shehu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yau alhamis, ya kai ziyarar aiki ta yini guda birnin Maiduguri na jihar Borno, inda bayan kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar, shugaban ya kuma gana da dakarun Sojin da ke yaki da Boko Haram a barikin Maimalari da ke zama shalkwatar yaki da ta’addanci a a shiyyar Arewa maso gabashin kasar. Daga Maiduguri, ga rahoton da wakilinmu Bilyamin Yusuf ya aiko mana.