Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace dalibai mata 30 a birnin Yauri na jihar Kebbi

Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta Kebbi ba ta ce uffan game da batun ba.
Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta Kebbi ba ta ce uffan game da batun ba. © Social News XYZ

Rahotanni daga Jihar Kebbi a Najeriya sun ce akalla dalibai 'yammata 30 'yan bindiga suka sace lokacin da suka kai hari makarantar Sakandaren mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri.

Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ce majiyoyi sun shaida mata cewar 'yan bindigar sun kai harin ne akan babura daga dajin Rijau da ke jihar Niger yau da asuba, inda suka fi karfin jami’an tsaron da ke gadin makarantar.

Jaridar ta ce majiyar ta ta shaida mata cewar bayan dalibai mata 30 da aka sace, 'yan bindigar sun kuma kwashi malamai guda 3 sun gudu da su.

Wannan shi ne hari na 3 da ake kai wa makarantun Najeriya a cikin makwanni 3 bayan wanda aka samu a makarantar Islamiyar Tegina a ranar 30 ga watan Mayu, wanda har yanzu ba’a kubutar da daliban ba da na makarantar fasahar Nuhu Bamalli da ke Jihar Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI