NAJERIYA-TSARO

Yan bindiga sun sace Yan kasar China dake aikin jiragen kasa

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin

Wasu Yan bindiga a Najeriya sun harbe dan sanda guda har lahira yayin da suka kwashi wasu Yan kasar China dake aikin gina layin dogo na zamani tsakanin Lagos da Ibadan.

Talla

Rahotanni sun ce Yan bindigar sanye da bakaken kaya sun yiwa ma’aikatan kofar rago ne a kauyen Alaagba dake kan iyakar Jihohin Oyo da Ogun inda suka yi awon gaba da su.

Rundunar Yan sandan Jihar Ogun ta tabbatar da aukuwar lamarin ta hannun kakakin ta Abimbola Oyeyemi wanda yace tuni aka baza jami’an tsaro domin farautar Yan bindigar.

Oyeyemi yace lamarin ya faru ne jiya laraba kuma ma’aikatan da Yan bindigar suka kwashe Yan kasar China ne dake aiki a tashar jiragen kasa dake Alaagba kusa da garin Kila.

Kakakin Yan Sandan ya tabbatar da mutuwar jami’in su dake tare da su lokacin aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.