Kebbi-'Yan bindiga

Mutanen Kebbi sun tunkari 'yan bindiga bayan sun fusata

Jami'an tsaron Najeriiya
Jami'an tsaron Najeriiya AP - Ibrahim Mansur

Bayanan da ke fitowa daga birnin Yaurin jihar Kebbi ta Najeriya na cewa al’ummar garin sun yi wa ‘yan ta’addar da suka sace dalibai kofar rago, bayan da suka fusata domin nema wa kansu mafita, yayin da aka yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar.

Talla

A zantawarsa da RFI Hausa, kwamandan ‘yan sintiri na jihar Kebbin da ke arewa maso yammacin Najeriya, Umar Hussaini Rambo, ya ce rashin daukar mataki daga gwamnati ne, ya tilasta wa mutanen garin yin fito-na-fito da ‘yan bindigar.

Daya daga cikin daliban kwalejin Yaurin ya rasa ransa sakamakon musayar wuya tsakanin sojoji da ‘yan bindigar da suka sace daliban.

Mataimakin Kwamandan Rundunar Hadin-Guiwa a yankin a shiyar arewa maso yammacin Najeriya, Air Commodore Abubakar AbdulKadir ya tabbatar da musayar wutar da aka yi tsakanin bangarorin biyu a yayin zantawarsa da manema labarai a Zamfara.

Jami’in ya cewa, an kuma yi nasarar kubutar da dalibai hudu  da malami guda daga hannun ‘yan bindigar.

‘Yan sandan jihar Kebbi sun bayyana cewa, ana ci gaba da aiki tukuru da zummar kubutar da sauran daliban da ‘yan bindigar suka sace a ranar Alhamis.

Har yanzu ba a tantance hakikanin adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba daga makarantarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.