Najeriya - Abuja - Kaduna

Masu zanga-zanga sun datse hanyar Abuja zuwa Kaduna

Yadda masu zanga-zanga suka datse babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Yadda masu zanga-zanga suka datse babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. © Daily Trust

Dubban mutane sun tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suke zanga-zangar neman gwamnati ta dauki matakan kawo karshen kashe mutane gami da yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa da ‘yan bindiga ke yi.

Talla

Majiyarmu ta ruwaito cewar tun da misalin karfe 7 na safiyar yau Asabar daruruwan mutane suka yi dandanzon rufe babbar hanyar, matakin da ya rutsa da matafiya da dama da suka makale.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro na kokarin lallaba masu zanga-zangar domin bude hanyar da suka datse.

Bayanai sun ce zanga-zangar ta biyo bayan karuwar hare-haren ‘yan bindigar akan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu yankunan da ke yankin, inda a baya bayan nan, wasu gungun ‘yan bindiga ska kashe wata karamar yarinya da shekarunta basu wuce 14 ba.

Lamarin dai ya auku ne Unguwar Magaji dake karamar Chikun inda maharan suka sace iyalan Mai Unguwa ko Dagacin garin tare da wani adadi na mazauna yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI