Najeriya - Tattalin Arziki

Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa amma da sauran Rina a Kaba - IMF

Wasu matasa a Najeriya yayin jiran samun damar aikin kwadago domin neman na kansu. 19/12/2018.
Wasu matasa a Najeriya yayin jiran samun damar aikin kwadago domin neman na kansu. 19/12/2018. © REUTERS/Afolabi Sotunde

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce tattalin arzikin Najeriya na farfadowa daga masassarar da ya shiga sannu a hankali, sai dai har yanzu ba ta sauya zani ba kan matsalolin da suka hada tsadar  kayayyaki da kuma karuwar marasa aikin yi.

Talla

Wata tawagar asusun na IMF karkashin jagorancin  Jemin rahman ce ta bayyana sakamakon binciken da ta gudanar, yayin ganawa da wakilan gwamnatin Najeriya ta kafar bidiyo a taron da suka yi daga 1 zuwa 8 ga watan Yuni.

Tawagar asusun na IMF ta ce matakan da hukumomin Najeriyar ke dauka dangane da daidaita darajar kudin kasar na Naira da canjin kudaden kasashen ketare na samun nasara, sai dai akwai bukatar daukar wasu karin matakai kafin cimma burin da ake bukata.

Wani mai sayar da kayayyakin masarufi a Najeriya.
Wani mai sayar da kayayyakin masarufi a Najeriya. © REUTERS/Temilade Adelaja

A makon da ya kare Bankin Duniya ya yi hasashen sake fuskantar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, abinda zai sa zuwa karshen wannan shekara, tashin farashin kayayyakin ya zama na 5 mafi kamari a yankin Kudu da Saharar Afrika, abinda ke nufin al’ummomin kasashen da suka hada da Zimbabwe, Zambia, Sudan ta Kudu da kuma Angola ne kawai za su fi na Najeriya fuskantar hauhawar farashin kayayyaki.

Hernandez, babban jami’in bankin duniyar ya kuma yi gagardin cewa hasashen nasu ya nuna tsadar farashin na kayayyakin bukata zai jefa karin ‘yan Najeriya miliyan 7 cikin kangin talauci, yayin da wasu miliyan 11 kari ka iya rasa guraben ayyukansu.

Rahoton Bankin Duniyar ya bayyana matsalolin tsaro, tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci ko addini da kuma tasirin annobar Korona a matsayin dalilan da suka haddasa kalubalen matsin tattalin arzikin ga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.