Najeriya - Coronavirus

An shafe makwanni 2 ba tare Korona ta kashe kowa a Najeriya ba

Wasu sanye da takunkuman rufe baki da hanci a birnin Abuja dake Najeriya.
Wasu sanye da takunkuman rufe baki da hanci a birnin Abuja dake Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce an shafe makwanni 2 curr ba tare da annobar Korona ta halakawa kowa ba a kasar.

Talla

Cikin sanawar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo cibiyar ta ce samun nasarar ya sanya har yanzu adadin wadanda cutar Koronar ta kashe a Najeriya tsayawa a mutane dubu 2 da 117.

Sai dai tayi gargadin cewa ana cigaba da samun masu kamuwa da cutar, inda a ranar Juma’ar da ta gabata aka gano karin mutane 13.

Sabbin alkaluman da cibiyar dakile yaduwar cutukan ta NCDC ta fitar sun nuna an yiwa mutane miliyan 2 da dubu 231 da 409 gwajin cutar Korona a Najeriya, yayin da mutane dubu 163 da 540 suka warke daga cikin dubu 167 da 155 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.