Gwamnonin Kudu maso Gabashin Najeriya sun nesanta kansu da IPOB

Gwamnonin jihohin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Gwamnonin jihohin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. © Daily Nigerian

Gwamnonin jihohin Kudu maso gabashin Najeriya sun Allah-wadai da masu fafutukar neman ballewa daga kasar, tare da nesanta kansu daga kungiyoyin na yankinsu da ma sauran dake wasu sassan Najeriyar.

Talla

Gwamnonin sun bayyana matsayar ta su ce, bayan ganawar da suka yi a garin Enugu, kan tashe-tashen hankulan da suka janyo hasarar rayuka da dukiya mai yawa a jihohin na Kudu maso gabashin Najeriya, sakamakon hare-haren ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biafra.

Daga cikin karin matakan da Gwamnonin suka zartas, akwai umartar matasan yankunansu da su kyale dattijai shiga gaba wajen neman hakkokinsu daga hukumomin Najeriya cikin ruwan sanyi, sai kuma kiran da suka yi ga kungiyoyin sauran yankunan Najeriya musamman na arewacin kasar da su kai zuciya nesa gami da baiwa kabilun Igbo mazauna yankunansu kariya daga duk wata barazana.

Baya ga gwamnonin jihohi, taron n agarin Enugu ya samu halartar ministan kwadago Chris Ngige, ‘yan majalisun tarayyar Najeriya, da na jihohin yankin na Kudu maso gabashi, sai kuma shugabannin kungiyar Ohaneze.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.