Najeriya - Benue

'Yan bindiga sun ji jiki a Neja da Benue

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. Finbarr O'Reilly/Reuters

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a Najeriya ta sanar da samun nasarar halaka ‘yan bindiga 14 a karshen mako, a lokacin da maharan suka kai hari kan ofishin ‘yan sandan dake karamar hukumar Katsin-Ala.

Talla

Cikin sanarwar da ta rabawa manema labarai a birnin Makurdi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Benue DSP Catharine Anene, ta ce ‘yan bindigar da adadinsu ya kai kimanin 50 sun afkawa ofishin ‘yan sandan na Katsina-Ala ne da zummar ceton ‘yan uwansu da ke tsare bayan kama su da aka yi jiya Asabar.

Kakakin ‘yan sandan ta ce suna cigaba da farautar ragowar ‘yan bindigar da suka tsere.

Za a iya cewa harin na baya bayan nan shi ne irinsa na farko da ‘yan bindiga suka kai a jihar ta Benue da zummar kubutar da ‘yan uwansu daga hannun ‘yan sanda.

Benue na daga cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma rikicin kabilanci lokaci zuwa lokaci, koda yake an samu saukin fadace-fadacen a watannin baya bayan nan.

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

A jihar Neja kuwa, rahotanni sun ce ‘yan bindiga kimanin 70 sun yi yunkurin afkawa yankin Unguwar Malam dake gaf da garin Kontagora, sai dai jami’an sojoji sun dakile yunkurin kai harin.

Jaridar Daily Trust da ke Najeriya ta ruwaito wani mazaunin garin da lamarin ya far una cewa sojoji sun samu nasarar kashe akalla 15 daga cikin ‘yan bindigar, a yayin da soja daya ya rasa ransa a fafatawar da suka yi da yammacin ranar jiya Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.