NAJERIYA-LAFIYA

Buhari ya fasa zuwa London domin duba lafiyar sa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya sauka a Abuja bayan ziyara a Faransa ranar 20 ga watan Mayun 2021.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya sauka a Abuja bayan ziyara a Faransa ranar 20 ga watan Mayun 2021. © Femi Adesina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da shirin tafiyar sa zuwa birnin London yau juma’a domin sake duba lafiyar sa kamar yadda fadar sa ta sanar cewar zai tafi yau.

Talla

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya gabatar tace an dage tafiyar zuwa wani lokaci nan gaba kuma za’a sanar da mutane idan lokacin yayi ba tare da karin bayani akai ba.

Babu dai wani Karin haske dangane da dalilin dakatar da tafiyar, kuma kokarin mu na samun karin bayani daga kakakin shugaban kasar Garba Shehu yaci tura.

Sanarwar shirin tafiyar shugaban Najeriya zuwa London jiya alhamis ta sake haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen kasar, inda masu suka ke cewa lokaci yayi da masu rike da mukaman gwamnati zasu inganta asibitocin da ake da su a gida domin daina tafiya zuwa kasashen waje dan kula da lafiyar su.

A bangare daya kuma masu goyan bayan shugaban na cewa babu wata dokar gwamnati da shugaban ya karya wadda ta hana shi tafiya inda yake so domin duba lafiyar sa.

Irin wannan tafiye tafiye a shekarar 2016 da 2017 sun haifar da fargaba da kuma mahawara tsakanin al’ummar kasar, yayin da bayan dawowar sa gida shugaba Buhari yace bai taba rashin lafiya irin wannan ba.

Jami’an gwamnati da kuma masu hannu da shuni sun mayar da tafiya kasashen Turai ko Asiya domin kula da lafiyar su a matsayin wata gasa saboda abinda suke kira rashin ingancin asibitocin gwamnati, yayin da kwararrun likitocin da ake da su a cikin kasar ke ficewa zuwa wasu kasashe saboda abinda suka kira rashin kular da ta dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.