Najeriya - Lafiya

Cutar Kwalara ta bulla a wasu jihohin arewacin Najeriya

An samu bullar cutar Kwalara ko Amai da gudawa a wasu jihohin Arewacin Najeriya, da suka hada Bauchi, Gombe, Kano, Plateau da Zamfara da kuma babban birnin tarayya Abuja, inda ya zuwa yanzu, akalla mutane dubu 6 da 500 ne suka kamu da cutar, yayin da 130 suka mutu.Daga Abuja Mohammad Kabir Yusuf ya aiko da rahoto kan halin da ake ciki.