NAJERIYA-LAFIYA

EFCC ta kaddamar da binciken almundahana akan Zenith Carex

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa ta EFCC AbduRashid Bawa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa ta EFCC AbduRashid Bawa © The Guardian Nigeria

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC ta kaddamar da bincike akan wani kamfanin kasar da ya aikata zamba cikin aminci na kudin da ya kai Dala miliyan 3 da suka shafi tallafin da Asusun Global Fund ke baiwa marasa lafiya a cikin Najeriya.

Talla

Ana zargin kamfanin da ake kira Zenith Carex da almundahana wajen kara alkaluman da suka shafi taimakon kudaden da ake bayarwa domin kula da masu fama da cutar kanjamau da tarin fuka da zazzabin cizon sauro da yawan su ya kai Dala miliyan 3.

Rahotan Global Fund yace kamfanin Zenith Carex ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019 kamar yadda binciken sa ya nuna wajen rubuta alkaluman magungunan da ake rabawa cibiyoyin kula da lafiyar dake sassan Najeriya.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar tace Hukumar EFCC ta tabbatar da kaddamar da bincike akan kamfanin Zenith Carex tare da wasu mutanen da ake zargin suna da hannu a cikin badakalar wanda ake fargabar zai taimaka wajen shafawa Najeriya kashin kaji.

Asibitin Koyarwar Aminu Kano
Asibitin Koyarwar Aminu Kano © Guardian Nigeria

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC tace tuni ta gana da shugabannin Global Fund akan wannan zargi da kuma kaddamar da bincike kamar yadda jami’ar Hukumar Elizabeth Ayodele tace anyi nisa akai.

Sai dai Kamfanin Zenith Carex da ya musanta zargin bayan yace ba zai ce komai akai ba domin yanzu haka maganar na hannun lauyoyin sa.

Asusun Global Fund yayi suna wajen karbar gudumawar kudade daga kamfanoni da masu bada agaji da kuma gwamnatocin kasashen duniya domin taimakawa marasa lafiya a kasashe matalauta ta hanyar samar musu da magunguna da kuma rigakafi kyauta ba tare da sun biya kudi ba.

Asibitin Koyarwar Obafemi Awolowo
Asibitin Koyarwar Obafemi Awolowo © Punch Nigeria

Global Fund kan yi amfani da kamfanoni a kasashen da yake gudanar da ayyukan sa domin ganin sun taimaka wajen samar da kayayyaki da kuma magungunan da ake bukata dan ganin sun kai ga cibiyoyin kula da lafiyar da za’a baiwa mabukata.

Daga shekarar 2003 zuwa yanzu Global Fund ya kashe kudin da ya kai Dala biliyan 2 a Najeriya wajen gudanar da irin wadannan ayyukan taimakawa marasa karfi samun magungunan da suke bukata.

Binciken da Global Fund ya sa aka gudanar akan ayyukan sa a Najeriya yace kamfanin Zenith Carex ya zambace shi kudin da ya kai Dala miliyan 3 ta hanyar hada baki da wasu bangarori da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.