NAJERIYA-TSARO

Rikicin Boko Haram zai hallaka mutane miliyan guda - MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Fabrice COFFRINI AFP/File

Majalisar Dinkin Duniya tayi hasashen cewar akalla mutane miliyan guda ke iya rasa rayukan su a Najeriya muddin aka ci gaba da rikicin boko haram nan da shekarar 2030, sakamakon karuwar hare haren da ake samu wadanda ke kai ga rasa dimbin rayuka.

Talla

Rahotan Hukumar ci gaba ta Majalisar yace ya zuwa karshen shekarar 2020 rikicin da aka kwashe shekaru sama da 10 ana yi yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 350,000 a jihohin Adamawa da Barno da kuma Yobe.

Daraktan Hukumar a Najeriya Mohammed Yahya ya bayyana matsalolin da aka samu daga bangaren talauci da karancin abinci da rasuwar yara kanana da rashin samun ilimi da tsaftacacen ruwan sha cewar ba zasu iya komawa kamar yadda aka saba ba nan da shekarar 2030 a yankin sakamakon illar da aka musu.

Tsohon shugaban boko haram Abubakar Shekau
Tsohon shugaban boko haram Abubakar Shekau Handout BOKO HARAM/AFP/Archivos

Yahya yace binciken da suka gudanar ya nuna cewar daga cikin kowanne mutum guda da ya jikkata sakamakon wannan rikicin wasu karin mutane 9 da suka hada da yaran makarantun firamare na rasa rayukan su saboda rashin abinci, yayin da sama da kashi 90 na mace macen da ake samu a rikicin na shafar yara ne masu kasa da shekaru 5.

Rahotan Majalisar yace illar da rikicin boko haram ya haifar ya lalata harkar kula da lafiyar al’ummar yankin da kuma hanyar samun abincin su da ya kai kasa da kashi 60 a jihohin Adamawa da Barno da kuma Yobe.

Yan gudun hijirar da rikicin boko haram ya shafa
Yan gudun hijirar da rikicin boko haram ya shafa REUTERS/Afolabi Sotunde

Yahya yace rashin zuba jari akan wadannan hanyoyin na dogon lokaci zai iya fadada rikicin zuwa wasu sassan Yankin Sahel, yayin da ya bukaci taimakon kasashen duniya da masu bada agaji wajen ganin an zuba jari na dogon lokaci da zai taimakawa Najeriya cimma muradun karnin da aka shirya zuwa shekarar 2063.

Rahotan ya bada shawarar cewar ya dace a mayar da hankali akan farfado da yankunan da wannan rikici ya yiwa illa ta hanyar hada kan al’umma ta da kuma samar musu da tsaro da tsarin shari’a da kuma farfado da hanyoyin more rayuwa da tattalin arziki da suka hada da makarantu da tashoshin Yan Sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.