NAJERIYA-TSARO

Za mu durkusar da tattalin arzikin Najeriya - Avengers

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS - Siphiwe Sibeko

Wata kungiyar mutanen da suka fito daga Yankin Naija Delta mai arzikin man fetur a Najeriya da ake kira ‘Niger Delta Avengers’ da tayi kaurin suna wajen kai hari akan bututun mai tana fasawa, ta sanar da dawowar ta da kuma aniyar ta na durkusar da tattalin arzikin Najeriya.

Talla

Kungiyar wadda tayi ta kai hare hare a farkon wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kaiga rage yawan man da kasar ke fitarwa daga ganga miliyan biyu da dubu 200 kowacce rana abinda ya kaiga jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki, ta sha alwashin kai munanan hare hare domin ganin ta karya tattalin arzikin Najeriyar.

Sanarwar da kungiyar ta gabatar wanda Jaridar Daily Trust ta wallafa yace zata kai hari kan Yan siyasar dake aiki da gwamnatin tarayya wajen yiwa Yankin Naija-Delta zagon kasa.

Kungiyar tace babu tantama Najeriya da tayi ta cin gajiyar arzikin man da ake samu daga yankin na gaf da rugujewa saboda matsalolin da suka hada da tsaro da ayyukan ta’addanci da na Yan bindiga a arewa da masu fafutukar raba kasa daga bangaren Oduduwa a Kudu maso Yamma da IPOB a Kudu maso Gabas, abinda ke nuna cewar a halin yanzu kwarya-kwaryar zaman lafiyar da ake samu a Yankin Kudu maso kudu ne ke ci gaba da rike kasar.

Kungiyar ta kara da cewa abin takaici shine duk da zama kashin bayan samar da tattalin arzikin Najeriya saboda kwanciyar hankalin da ake da shi wajen hakar mai da fitar da shi da manyan kamfanonin duniya ke yi domin amfani da kudin da ake samu wajen tafiyar da kasa, Yankin Naija Delta da Kudu maso kudu ya kasance koma baya wajen ci gaba, yayin da ake watsi da bukatun sa.

Ma'aikacin mai a matatar man Fatakwal
Ma'aikacin mai a matatar man Fatakwal Photo: AFP/Pius Utomi Ekpei

Avengers tace ta yanke hukuncin dakatar da yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa a shekarun baya saboda ganin yadda ya jefa Najeriya cikin masassarar tattalin arziki shekaru 4 da suka gabata wanda suka yi saboda sauraran shugabannin su wadanda suka bukaci baiwa gwamnati lokaci domin aiki akan bukatun su.

Kungiyar tace yanzu zata kaddamar da sabbin hare hare saboda gwamnati ta gaza wajen cika alkawarin da ta musu.

Bututun man matatar Dangote dake Lagoscapital Lagos June 25, 2016.
Bututun man matatar Dangote dake Lagoscapital Lagos June 25, 2016. Reuters/路透社

Kungiyar ta kuma bayyana rashin amincewar ta da jagorancin Chief Edwin Clarke da kungiyar sa ta PANDEF, yayin da ta bayyana kaddamar da shirin da ta yiwa suna ‘Operation Humble’ da zummar kai hari kan duk wasu bututun mai dake Yankin Naija Delta domin ganin kasar ta afka cikin matsalar tattalin arziki.

Avengers tace babu wani bututun mai da zata bari yana aiki a yankin, yayin da ta bukaci matasan ta da su zauna cikin shirin ko ta kwana domin karbar umurni, a daidai lokacin da tace tana fatar gwamnatin Najeriya zata sake tunani domin biya musu bukatun su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.