Najeriya - Maiduguri

Zulum ya dakatar da kungiyar agajin Faransa saboda koya wa mutane harbi

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum RFI Hausa / Ahmad Abba

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum ya dakatar da wata kungiyar agaji dake zaman kanta mai suna ACTED daga kasar Faransa.

Talla

Gwamnan ya dauki matakin ne bayan da a yau Asabar bincike ya bankado yadda kungiyar mai zaman kanta ke amfani da wani Otal a birnin Maiduguri wajen baiwa wasu mutane horo kan koyon harbi.

Yayin sanar da matakin dakatarwar, kakakin gwamnan na Borno Malam Isa Gusau, yace kungiyar bada agajin ta Faransa na amfani da bindigogin roba wajen baiwa mutane horon harbin.

A cewar Gusau asirin mutanen ya tonu ne, bayanda wasu mazauna kusa da Otal din a Maiduguri suka rika jiyo karar harbin bindiga daga cikin Otal din, abinda ya sanya ‘yan sanda kai samame, inda suka kame mutane biyu dake jagorantar bada horon dukkaninsu ‘yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.