NAJERIYA-SIYASA

Gwamnan Zamfara Matawalle ya fice daga PDP - Ahmed

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle premiumtimesng

Gwamnan Jihar Zamfara dake Najeriya Bello Matawalle ya bi sahun wasu jiga jigan ‘yayan babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a kasar wajen sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki bayan daukar dogon lokaci ana rade radi akai.

Talla

Wannan sauya sheka ya biyo bayan sanarwar da mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin yada labarai Bashir Ahmed yayi a shafin sa na Facebook kamar yadda kafofin yada labaran Najeriya suka ruwaito.

Rahotanni sun ce Gwamnan ya dade yana nuna alamun barin Jam’iyyar PDP da ta bashi damar hawa karagar mulki amma kuma yaki furta komai dangane da shirin.

A cikin wannan wata tawagar Gwamnonin Jam’iyyar APC da PDP sun ziyarci Jihar Zamfara inda suka gana da shi dangane da matsalolin tsaron dake ci gaba da yiwa jihar sa illa da kuma batun sauya shekar kamar yadda ake ta hasashe.

Wata majiya daga shugabannin Jam’iyyar APC a Jihar tace a ranar talata mai zuwa za’a gudanar da gagarumin bikin karbar Gwamnan a birnin Gusau domin tabbatar da ficewar sa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Matawalle ya zama Gwamnan Jihar Zamfara ne sakamakon hukuncin kotun koli a shekarar 2019 wadda tace Jam’iyyar APC da ta lashe zaben da akayi a Jihar bata da halartattun Yan takara a matakai daban daban saboda kasa gudanar da zaben fidda gwani.

Sauya shekar Matawalle zuwa APC na iya sauya akalar siyasar Jihar Zamfara lura da cewa akasarin Yan adawar Jihar na cikin Jam’iyyar ce musamman tsohon Gwamnan Jihar Abdul’aziz Yari rahotanni suka ce basa ga maciji da juna.

Wannan shine karo na biyu da Jam’iyyar PDP ke asarar kujerun Gwamnonin ta bayan da a watannin baya Gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi da takwaran sa na Cross Rivers Ben Ayade suka fice daga cikin ta zuwa Jam’iyyar APC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.