Najeriya-INEC
INEC ta fara rijistar 'yan Najeriya don tunkarar zaben 2023
Wallafawa ranar:
A yau ne Hukumar zaben Najeriya ta sake bude rumfunanta domin cigaba da yin rijistar 'yan kasar, ta hanyar yin amfani da yanar Gizo, a shirye-shiryenta na tunkarar zaben 2023 mai zuwa. A cewar Hukumar, ta na sa ran yi wa mutane akalla miliyan 20 rijista cikin shekara guda. A wani yunkuri na ganin 'yan kasar miliyan 100 su na da rijistar kafin zaben na 2023. Daga Abuja ga rahoton Kabir Yusuf.