NAJERIYA-SIYASA

APC ta mika ragamar Zamfara hannun Gwamna Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle © Governor Matawalle

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle a matsayin jagoran ta a Jihar bayan sauya shekar da yayi daga Jam’iyyar PDP a wani gagarumin bikin da aka yi a Gusau wanda ya samu halartar jiga-jigan ta na kasa.

Talla

Shugaban Jam’iyyar APC na riko kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyana haka wajen bikin bayan ya sanar da rusa shugabannin Jam’iyyar a Jihar daga matakin unguwanni zuwa Jiha.

Buni ya bukaci daukacin ‘yayan Jam’iyyar APC dake Jihar Zamfara da su baiwa Gwamna Matawalle goyon baya a matsayin sa na sabon shugaban su wajen ganin sun yi aiki tare domin samar mata da jihar ci gaba.

Yayin jawabin sa wajen taron, tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari yace ya amince da matsayin da Jam’iyyar ta kasa ta dauka kuma a shirye yake ya baiwa Gwamna Matawalle goyan bayan da yake bukata.

Yari ya bukaci Gwamnan da yayi taka tsan tsan da wadanda ya bayyana a matsayin munfukai dake hana ruwa gudu wajen hada kan jama’a.

Gwamna Matawalle yace a matsayin sa na shugaba zai tabbatar da yin adalci ga kowanne bangare na ‘yayan jam’iyyar ta su.

Bikin karbar Gwamna Matawalle ya samu halartar Gwamnonin Jihohin Borno da Katsina da Ogun da Plateau da Kano da Kogi da Kaduna da Jigawa da Niger da kuma Kebbi tare da Sakataren Gwamnatin tarayya da ministoci da Yan Majalisun Dattawa da na wakilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.