Najeriya-Biafra

Gwamnatin Najeriya ta kamo jagoran Biafra Nnamdi Kanu daga ketare

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kame jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB Nnamdi Kanu wanda ya tsere daga kasar tun cikin shekarar 2017 bayan bayar da belinsa daga shari’ar da ya ke fuskanta kan cin amanar kasa.

Talla

Ministan shari’ar kasar Abubakar Malami ya bayyana kama Kanu a wani taron manema labarai, inda zai ci gaba da fuskantar tuhumar cin amanar kasa da kuma jagorancin haramtacciyar kungiyar da ke neman raba kasar.

A watannin da suka gabata ‘ya'yan kungiyar sa sun yi ta kai hare hare tashoshin 'yan Sanda da gidajen yari a jihohin kudu maso gabas inda su ke kashe jami’an 'yan Sanda da kuma sakin fursinoni.

Rahotanni sun ce akalla 'yan Sanda 150 'yan bindigar da ake zargin magoya bayan kungiyar sa suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.