NNPC-Najeriya

NNPC ya sanar da bukatar kara farashin mai zuwa sama da 280

Matatar man fetur mallakin NNPC a Najeriya.
Matatar man fetur mallakin NNPC a Najeriya. Africanews

Shugaban Kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya Mele Kyari ya ce ya dace a dinga sayar da litar mai guda akan sama da naira 280 saboda wahalar da ake yi wajen sarrafa shi da kuma samar da shi ga jama’a.

Talla

Kyari wanda ya ce yanzu haka gwamnatin kasar na tattaunawa da shugabannin kungiyoyin kwadago dangane da farashin man da kuma yadda ya dace a sayarwa jama’a, ya ce gwamnati na sanya kudade sosai wajen ganin jama’ar kasa sun samun man cikin farashi mai sauki.

Shugaban kamfanin NNPC ya ce babu wata kasa a duniya da ta ke sayar da man dizil da manyan motoci da injina ke amfani shi fiye da farashin man fetur kamar yadda ake yi yanzu a Najeriya inda ake sayar da lita guda na dizil akan naira 280, yayin da kuma ake sayar da fetur akan naira 162.

Kyari yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya basu umurnin daukar matakan da suka dace na tabbatar da cewar ba’a kara farashin man yadda zai gagari talakawa ba musamman a wannan lokaci.

Jami’in ya ce wannan umurni ya nuna cewar za su dinga amfani da wasu kudaden da ya dace a yiwa jama’a aiki da su wajen sanya tallafin da gwamnati ke zubawa domin daidaita farashin man.

Shugaban kamfanin da yace babu wata alama na kara farashin man a watan Yuli mai kamawa yayi zargin cewar fasa kwabrin man da ake yiwa zuwa kasashen makota na daga cikin dalilan dake nuna yawan man da ake amfani da shi a cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.