NAJERIYA-TSARO

Yan bindiga sun kashe Dan Majalisar Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle © Premiumtimes

Yan bindiga a Najeriya sun harbe ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Zamfara Mohammed Ali Ahmed har lahira lokacin da yake tafiya akan hanyar Gusau zuwa Funtua dake Jihar Katsina

Talla

Babban jami’n dake kula da Majalisar dokokin Jihar Saidu Anka ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya jefa jama’ar Jihar cikin wani sabon tashin hankali.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala bikin karbar Gwamnan Jihar Bello Matawalle da wasu Yan majalisu da suka sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Bayanai daga Jihar sun ce Yan bindigar da suka harbe Dan Majalisar sun kuma kama 'dan sa da direban sa wadanda ke hannun su yanzu haka.

Jihar Zamfara ta kwashe shekaru tana fama da matsalar Yan bindiga dake kai hari suna kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba.

Kokarin gwamnati na shawo kan matsalar ya faskara ganin yadda ta fadada zuwa wasu jihohin dake makotaka da ita irin su Kaduna da Katsina da Niger da kuma Kebbi da kuma Sokoto.

Gwamna Bello Matawalle yayi kokarin sasantawa da Yan bindigar domin ganin sun aje makaman su amma abin yaci tura, yayin da wasu daga cikin wadanda suka rungumi shirin suka sake daukar makamai.

Ko a makwannin da suka gabata sanda Gwamnan ya dakatar da wasu Sarakuna da ake zargin suna taimakawa Yan bindigar wadanda ke kashe mutane suna sace dukiyoyin su

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.