Najeriya

Masu fasakaurin shinkafa sun raunata jami'an kwastana a Najeriya

Shugaban hukumar kwastan a Najeriya Hameed Ali.
Shugaban hukumar kwastan a Najeriya Hameed Ali. guardian.ng

Akalla jami’an kwastan 3 da wani soja daya ne suka ji rauni sakamakon wani hari da masu fasakaurin shinkafa suka kai musu a yankin Igboora dake karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a Najeriya.

Talla

Kakakin hukumar kwastan a kasar, Theophilus Duniya, ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya raba wa manema labarai a jiya Asabar, inda ya ce lamarin ya auku  ne da misalin karfe 8 na daren Juma’a.

Ya ce jami’an da suka ji raunin sun hango manyan motoci 8 makare da shinkafa ‘yar waje ne, amma kafin su kai ga  daukar mataki, wadanda ke cikin motar suka far musu da bindiga.

Sai dai jami’an sun yi nasarar harbe daya daga cikin masu fasakaurin, a yayin da sauran suka koma da kayan da suka dauko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.