Najeriya - Benin

Kokarin dawo da Sunday Igboho daga Benin na neman gamuwa da cikas

Sunday Adeyemo, mai ikirarin kare hakkin Yarabawa a Najeriya.
Sunday Adeyemo, mai ikirarin kare hakkin Yarabawa a Najeriya. © twitter

A Najeriya, kokarin dawo da mai rajin kafa Kasar Yarabawa, Sunday Ade Adeyemo da akafi sani da  Sunday Igboho wanda Mahukuntan kasar Benin suka cafke kan hanyarsa ta gudu zuwa Kasar Jamus na neman gamuwa da cikas, sakamakon wani yunkuri da aka ce wasu shugabannin Yarabawa na yi  don hana faruwar hakan. Dangane da abinda suka kira yunkuri ne da baya cikin yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kasar ta Benin a shekarar 1984.

Talla

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahotan daga wakilin mu na Abuja Mohammed Kabir Yusuf .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.