'Yan bindiga sun saki mutane 100 a jihar Zamfaran Najeriya

Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Zamfara a Najeriya ya daidaita
Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Zamfara a Najeriya ya daidaita RFIHAUSA

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da sakin mutane dari daya da ‘yan bindiga suka kwashe a garin Manawa da ke jihar Zamfara, bayan share tsawon kwanaki 42 ana garkuwa da su.

Talla

A sanarwar da ta fitar yammacin ranar talata, rundunar ‘yan sandan ta ce mutanen 100 da suka hada da mata, da maza, da kananan yara wadanda aka kwashe ranar 8 ga watan yunin da ya gabata dukanninsu an sake su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara Mohammed Shehu, ya ce an saki mutanen ne ba tare da an gindaya wani sharadi ba, sannan ya ce ba a biya kudin fansa ba.

Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar matsalar ‘yan bindiga da ke yin garkuwa da mutane da kuma neman a biya su kudaden fansa, yayin da a wasu lokutan ‘yan bindigar ke afka wa garuwa tare da kashe jama’a.

A ranar litinin da ta gabata ma ‘yan bindigar sun kashe ‘yan sanda 13 a jihar ta Zamfara a daidai lokacin da suke kan hanyar kai wa jama’a dauki sakamakon farmakin ‘yan bindiga da ake kira barayin shanu da masu garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.