Najeriya-Ta'addanci

Jiragen yakin Najeriya sun iso kasar daga Amurka

Samfurin jiragen yakin da Najeriya ta yi oda daga Amurka domin ragargazar 'yan ta'addan da ke addabar kasar.
Samfurin jiragen yakin da Najeriya ta yi oda daga Amurka domin ragargazar 'yan ta'addan da ke addabar kasar. embraerdefensesystems.com/

Shida daga cikin jiragen yaki 12 da Najeriya ta yi oda tun a watan Afrilun shekara 2018 daga Amurka, sun isa kasar a daren da ya gabata, mako guda bayan harbo mata wani jirgin yakin da 'yan bindiga suka yi a jihar Zamfara.

Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Muhammad Kabir Yusuf daga birnin Abuja

 

Jiragen yakin Najeriya sun iso kasar daga Amurka

 

 

Jiragen yakin sun iso ne a wani lokaci da kasar ke bukatar su, ganin yadda aikace-aikacen  'yan ta'adda ke kara kamari a gabashi da yammacin arewacin kasar.

Masharhanta irinsu Group Captain Saddig Shehu Garba mai ritaya na cewa, wadannan jirage na da matukar amfani dangane da fafutukar da Najeriya ke yi na ganin ta kakkabe ayyuakan tsage a kasar.

Kafin zuwan wadannan jiragan, Najeriyar ta rasa jiragan yakinta har guda hudu a yakin da ta ke yi da 'yan ta'adda, amma masana harkokin tsaro na diga ayar tambaya kan musabbabin salwantasu.

Kodayake gwamnatin Najeriya na shan jinjina kan yadda ta sayo jiragen, abin da ya sa wasu 'yan kasar ke cewa, lallai gwamnatin da gaske take a yakin da take yi da 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.