Najeriya

Najeriya ta daure ‘yan fashin teku shekaru 12 kan satar jirgin ruwa

Sojojin ruwan Najeriya dake samun horos kan dakile fashin taeku.
Sojojin ruwan Najeriya dake samun horos kan dakile fashin taeku. AFP

A Najeriya wata kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 12 kan wasu 'yan fashin teku 10 da suka sace wani jirgin ruwan kamun kifi na kasar China da kuma matukansa a watan Mayun shekarar da ta gabata.

Talla

Rundunar sojin ruwan kasar tace, wannan shi ne hukunci irinsa na biyu karkashin sabuwar dokar fashin teku.

'Yan fashin, dukkansu' yan Najeriya ne, an same su da laifin satar jirgin ruwan kasar China FV Hailufeng II a Tekun Guinea a shekarar 2020.

Hare-haren satar mutane kan jiragen ruwa domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare a tekun Guinea, wanda ke tashi daga Senegal zuwa Angola, har ya kai yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Alkali Ayokunle Faji na Babban Kotun Tarayya da ke Legas ya ce an yanke hukuncin ne domin hakan ya zama izini ga wasu.

Kazalika alkalin babbar kotun ya umarci mutanen da aka samu da laifi su biya tarar naira dubu 250 ko wannen su wato $610.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.