Najeriya-Buhari

Najeriya ta yi dacen samun Buhari a matsayin shugaba - Sarkin Daura

Sarki Daura Faruk Umar Faruk
Sarki Daura Faruk Umar Faruk @Opera

Sarkin Daura a jihar katsina Alhaji Umar Faruk Umar, ya ce Najeriya ta yi dacen samun Muhammadu Buhari a matsayin  shugaba a daidai wannan lokaci da ta ke fuskantar kalubale.

Talla

Ya ce ba don Buhari ne shugaban Najeriya ba a yanzu, al’amura za su rincabe sosai, yana mai cewa zai yi matukar wahala a samu damar taruwa a fadarsa.

Sarkin ya kara da cewa, al’ummar Daura sun ce moriyar kasancewar Buhari shugaban kasa, duba da yadda daidaikun mutane da kungiyoyi ke zuwa musu da ababen more rayuwa.

A nasa jawabin, Buhari ya bayyana farin cikinsa da kasancewa a mahaifarsa, inda ya yi tuni da yadda yake ziyartar fadar sarkin Daura a matsayinsa na shugaban mulkin soja a shekarun baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.