Najeriya-'Yan bindiga-Katsina

'Yan sanda sun ceto mutane 8 daga masu garkuwa a Katsina

Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba

A Najeriya ‘yan sanda sun dakile wani harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Kabobi da ke karamar hukumar Batasari a jihar Katsina.

Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Juma’ar nan.

Ya ce da misalin karfe 2 da rabi na rana ne dimbim ‘yan bindigar suka shigo garin isa babura, rike da bindigogi kirar AK 47, kuma suka datse hanyar da ta tashio daga Jibia zuwa Batsari, inda suka yi awon gaba da ilahirin fasinjojin da ke cikin wata motar Volskwagen  Passat da suka tare.

Da jin haka ne  babban jami’ain ‘yan sandan Batsari ya jagoranci tawagar Operation Puff Adder da Sharan Daji zuwa dajin da ‘yan bindigar suka shiga, kuma suka ceto mutane 8 bayan sunyi bata kashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.