Najeriya-'Yan bindiga-Tegina

Daliban Tegina na hannun 'yan bindiga duk da an biya su Naira miliyan 30

Daya daga cikin ajizuwan makarantar Islamiyyar da aka sace daliban Tegina.
Daya daga cikin ajizuwan makarantar Islamiyyar da aka sace daliban Tegina. - AFP

‘Yan bindigar da suka sace daliban makarantar Islamiyya 150 ta Tegina a jihar Neja na rike da su har yanzu duk da biyansu kudin fansa har naira miliyan 30  da aka yi, kamar yadda bincike da jaridar Daily Trust da ake wallafa wa a kasar ya nuna.

Talla

A ranar 30 ga watan Yuni ne aka sace wadanna yara, wanda bayan haka ne ‘yan bindigar suka nemi a biya kudin fansa har naira miliyan 200 kafin su sake su, amma suka rage kudin zuwa naira miliyan 50 bayan magiya da aka yi musu.

Sai dai gwamnatin jihar Neja ta zake cewa ba za ta biya kudin fansa ba.

Binciken ya nuna cewa iyayen yaran da suka rasa na yi sun rugumi kaddara, inda suka koma neman taimako a masallatai da coci coci.

Majiyoyi da dama a garin na Tegina sun ce  iyayen sun samu ikon tara naira miliyan 30 ta wajen roko da sayar da kadarorinsu, kuma kwanaki biyu da suka wuce suka mika wa ‘yan bindigar, amma  ba su saki yaran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.