Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun saki 28 daga cikin dalibai 121 da suka kwashe a Kaduna

Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara.
Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara. AP - Ibrahim Mansur

‘Yan bindigar da suka kwashe dalibai 121 a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya a farkon watan Yulin nan sun saki 28 daga cikinsu, kamar yadda wani babban jami’in makarantar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP wannan Lahadi.

Talla

Joseph Hayab ya ce daga cikin daliban Bethel Baptist High School da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, 34 sun kubuta, yayin da 81 ke hannun ‘yan bindigar.

Harin da aka kai makarantar sakandaren Bethel Baptist High School ta Kaduna shi ne  irinsa na 10 a arewa maso yammacin Najeriya tun daga watan Disamba.

Hukumomin Najeriya sun danganta irin wannan satar mutane da neman kudin fansa daga ‘yan bindiga.

Kokarin samun rundunar ‘yan sanda da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna don karin bayani ya ci tura.

Radika Bivan, wata uwa wadda ‘yar ke cikin wadanda aka sace ta tabbatar da sakin 28 daga cikinsu, amma ta ce babu ‘yar ta a cikin wadanda suka kubuta.

Tuni gwamnatin Kaduna ta bada umurnin rufe makarantar da wasu 12 a jihar, biyo bayan aukuwar satar daliban, ba tare da fadin ranar da za  asake bude su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.