Najeriya-'Yan bindiga-Katsina

'Yan bindiga sun saki 4 daga wadanda suka dauka a Katsina matsayin goron Sallah

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

A Najeriya ‘yan bindiga sun saki 6 daga cikin mutane 28 da suka shafe kwanaki 67 su na garkuwa a da su a jihar Katsina, su na mai cewa sun saki 4 daga cikin su ne a matsayin goron Sallah.

Talla

A kwamnakin baya ne dai jaridaar Premium Times da ake wallafawa  Najeriya ta buga labarin da ke cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dan kasuwa, kana suka yi awon gaba da mutane 28 a garin Batsari.

Amma majiyoyi daga yankin na cewa da yammacin Juma’a ‘yan bindigar suka aike musu da sakon cewa za su saki wata mata da danta, bayan da mijinta ya biya kudin fansa  har Naira miliyan 2 da rabi.

Sai dai kuma wata majiyar ta ce a yayin da suke sakin matar da danta ne suka yanke shawarar sakin wasu mutane 4 a matsayin goron sallah ga al’ummar garin na Batsari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.