Kaduna-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sake sace basarake a Kaduna

Jami'an tsaron Najeriya
Jami'an tsaron Najeriya REUTERS/Stringer

‘Yan bindiga sun sake sace wani basaraken gargajiya a jihar Kadunan Najeriya, mai martaba Jonathan Danladi Gyert Maude da ake yi wa kirari da Kpop Ham na Jaba.

Talla

‘Yan bindigar sun sace shi ne a jihar Nasarawa kamar yadda rahotanni ke cewa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa, an sace sarkin ne a yankin Panda na jihar Nasarawa bayan ya ziyarci wata gonarsa.

Wannan na zuwa bayan makwanni biyu da ‘yan bindigar suka sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu duk dai a Kadunan.

Kodayake an saki Sarki Alhassan bayan ya shafe tsawon sa’o’i 24 a hannun ‘yan bindigar, amma har yanzu iyalansa 13 na hannunsu.

‘Yan bindigar sun bukaci a biya su fansar Naira miliyan 200 kafin sakin mutanen da suka tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.