Najeriya-Kaduna

Don Allah 'yan bindiga ku tausaya wa Sarkin Jaba-Fasto Buru

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria

Fitaccen jagoran addinin Kirista a Najeriya, Fasto Yohanna Buru ya roki 'yan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Jaba na Kaduna, Mai Martaba Jonathan Danladi Maude da su yi wa Allah su sake shi, duba da shekarunsa da kuma matsayinsa na shugaban al'umma.

Talla

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Fasto Buru wanda da ne ga Sarkin ya bayyana cewa, Sarkin ba shi da juriyar shan wahala, la'akari da cewa, ya haura shekaru 80.

A yayin rokan 'yan bindigar, Fasto Buru ya  musu,

Ku yi hakuri, ku dubi shekarun wannan dattijon, ku dubi girmar haihuwa da kuma matsayinsa na shugaban al'umma, mutumin da ke da shekaru akalla 83, ba shi da karfin juriya kan abin da zai faru da shi.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren kalaman Fasto Buru

 

Don Allah 'yan bindiga ku tausaya wa Sarkin Jaba-Fasto Buru

 

 

‘Yan bindigar sun sace shi ne a jihar Nasarawa kamar yadda rahotanni ke cewa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa, an sace sarkin ne a yankin Panda na jihar Nasarawa bayan ya ziyarci wata gonarsa.

Wannan na zuwa bayan makwanni biyu da ‘yan bindigar suka sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu duk dai a Kadunan.

Kodayake an saki Sarki Alhassan bayan ya shafe tsawon sa’o’i 24 a hannun ‘yan bindigar, amma har yanzu iyalansa 13 na hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.