Najeriya-Kwalera

Kwalera ta kashe mutane 479 a Najeriya

Mutane da dama na kwance a asibiti bayan kamuwa da cutar kwalera
Mutane da dama na kwance a asibiti bayan kamuwa da cutar kwalera Reuters/St-Felix Evens

A jumulce, mutane 479 suka rasa rayukansu sakamakon annobar kwalera da ta yadu a jihohin Najeriya akalla 18 kawo yanzu.

Talla

Cibiyar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa ta Najeriya NCDC ta bayyana haka a wani sabon rahoton da ta fitar.

Cibiyar ta ce, tun daga farkon wannan shekara, jumullar mutane dubu 19 da 305 suka harbu da cutar, yayin da ta bazu a jihohin kasar 18 da suka hada da birnin tarayya Abuja.

Jihohin sun hada da Benue da Delta da Zamfara da Gombe da Bayelsa da Kogi da Sokoto da Bauchi da Kano da Kaduna.

Sauran sun hada da Filato da Kebbi da Cross River da Niger da Jigawa da Yobe da Kwara da kuma birnin Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.