Benin -Najeriya

Za a ci gaba da tsare Igboho a gidan yarin Jamhuriyar Benin

Sunday Igboho, shugaban masu neman kasar Oduduwa.
Sunday Igboho, shugaban masu neman kasar Oduduwa. © The Cable

Alkali a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin ya bayar da umurnin tsare dan Najeriya Sunday Igboho jagoran masu fafutukar kafa kasar Yarbawa zalla a gidan yarin kasar, tare da sanar da shi sabbin laifukan da ake zargin shi da aikatawa.

Talla

A yanzu dai kotu na zargin Sunday Igboho ne da hada baki da wani gungun batagari don aikata miyagun laifufuka a cikin kasar ta Benin, a maimakon zarge-zargen da aka gabatar masa da farko ranar alhamis da ta gabata, wadanda suka hada da batun mallakar makamai da kuma tunzura jma’a don yi wa kasarshi Najeriya tawaye.

To sai sai lauyoyin Igboho sun bayyana matukar mamakinsu a game da sabon zargin, inda suke cewa ta yaya za’a tuhume shi da hada baki da gungun batagari don aikata aikata miyagun laifufuka a Benin alhali an cafke shi ne kasa da sa’o’i bayan shigar shi a kasar.

Lauyoyin Igboho sun ce a daya bangare sun gamsu da yadda shari’ar ke tafiya, lura da cewa za a a tsare wanda suke karewa ne a gidan yarin jamhuriyar Benin maimakon a Najeriya inda suka ce ba su da tabbacin abinda zai faru da shi idan aka tasa keyarsa zuwa can.

Wakilin radio France international a birnin Cotonou Jean-Luc Aplogon ya ce har zuwa yanzu ba inda alkalan kotun suka bayyana cewa Najeriya na bukatar a tasa mata keyar Sunday Igboho don ya fuskanci shari’ar a gida ba amma  wasu bayanai sun ce kasar ta yi hakan a asirce.

Magoya bayan Igoho da dama ne suka taru a harabar kotun da ke birnin Cotonou a zuwa daren jiya, kafin su bar wurin bisa umarnin jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.