Najeriya

Kotun Najeriya ta umurcin saki masu fafutukar nuna adawa da Buhari

Shugaban Najeriya,  Muhammadu Buahri.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buahri. REUTERS - Siphiwe Sibeko

Kotun Najeriya ta umurcin rundunar ‘yan sandan DSS ta saki mutane biyar da ta kama saboda sun sanya riga mai dauke da alamun nuna adawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari kamar dai yadda lauyan mutanen Allen Sowore ya sanar.

Talla

An dai kame mutanen ne a farkon watan yuli a cikin wata mujami’a da ke Abuja saboda kowannensu na sanye da rigar da a jikinta aka rubuta "Buhari Must Go!" da ke nufin ‘’Dole ne Buhari ya sauka’’.

Hukumar gudanarwa ta wannan mujami’a ta musanta zargin cewa ta taka rawa don cafke mutanen biyar, yayin da a ranar litinin babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin sakin mutanen ba tare da wani sharadi ba.

To sai dai lauyansu Sowore, ya ce har zuwa marecen ranar talata kotun ba ta ba su takardar da za su gabatar wa hukumar DSS domin sallamar mutanen ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.