Najeriya-Tattalin Arziki

Najeriya ta daina sayar wa ‘yan canji kudaden ketare

Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja dake Najeriya. 22/1/2018.
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja dake Najeriya. 22/1/2018. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu ya daina sayar wa ‘yan canji masu lasisi wato Bureaux de Change kudaden ketare kamar yadda ya saba saboda zargin rashawa da kuma damfara da yake yi wa ‘yan canjin.

Talla

Gwamnan Babban Banki Gowin Emefiele, ya zargi ‘yan canjin da cewa a maimakon gudanar da harkokinsu na kasuwanci, a yanzu sun rike zuwa masu taimakawa don yada rashawa a cikin harkokinsu.

Emefiele ya ci gaba da cewa ‘yan canjin na taimaka wa masu gudanar da mummunar harkalla da kuma halasta kudaden haram a Najeriya, tare da alkawarin daukar mataki a kan masu aikata hakan.

Shugaban CBN wanda ke gabatar da jawabi a karshen taron Kwamitin Tsara Siyasar Kudade na kasar (MPC)  a birnin Abuja, ya ce daga yanzu ba za a sake sayar wa ‘yan canjin kudaden ketare ba kamar yadda aka saba balantana sayar masu da sabon lasisi don gudanar da harkokinsu.

Godwin Emefiele ya ce a maimakon Bureax de Change, yanzu CBN za ta yi hulda ne kai-tsaye da bankunan kasar tare da tabbatar da cewa an samar da kudaden ketare a wadace ga wadanda ke shigar da kayayyaki daga ketare zuwa cikin kasar, da sayen magunguna, biyan kudaden makaranta, yin tafiye-tafiyen da ba su saba wa doka ba da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.