ZABE-KOTU

Najeriya: kotu ta kalubalanci sahihancin zaben gwamnan Ondo.

Shuwagabanin Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshoimhole daga  hagu, sai Alhaji Bola Ahmed Tinubu daga dama.
Shuwagabanin Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshoimhole daga hagu, sai Alhaji Bola Ahmed Tinubu daga dama. PM News Nigeria

Takaddama ta kaure game da halascin kwamitin rikon jagorancin jam`iyyar APC  mai mulkin Najeriya, bayan wani hukuncin Kotun Koli, kan rashin halacin gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, da dan takarar jam`iyyar PDP ya kalubalanci sahihancin zabensa.Hukumcin kotun dai ya ce,  kwamitin rikon jam`iyyar da ya tabbatar da shi takarar haramtacce ne.Ga wakilinmu na Abuja Mohammed Sani Abubakar dauke da rahoto.